Home Labaru Nnamdi Kanu Ya Roƙi Magoya Bayan Sa Kada Su Tada Hayaniya A...

Nnamdi Kanu Ya Roƙi Magoya Bayan Sa Kada Su Tada Hayaniya A Kotu

50
0

Shugaban Kungiyar masu Rajin Neman Kafa Ƙasar Biafra Nnamdi Kanu, ya roƙi magoya bayan sa cewa kada su tada hankali a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja idan an je shari’ar sa a mako mai zuwa.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 18 ga watan Janairu ne Mai Shari’a Binta Nyako za ta yanke hukuncin ko Nnamdi Kanu ya na da gaskiya ko za a cigaba da shari’ar sa.

Yayin da ake shirin zaman kotun, lauyan Nnamdi Kanu Ifeanyi Ejiofor, ya same shi a Helkwatar tsaro ta SSS da ke Abuja su ka tattauna yadda zaman kotun zai kasance.

Lauya Ejiofor ya sanar cewa, Nnamdi Kanu ya na gaida ɗimbin magoya bayan sa na ciki da wajen Nijeriya, amma ya yi roƙon cewa kada su tada hankali a harabar Kotun idan an je sauraren shari’ar.