Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC, ta haramta wa ɗaukacin
shugabannin ta da sauran jami’an majalisar ta na jihohin
Nijeriya bada kyaututtuka ga ‘yan siyasa.
NLC, ta ce za ta ɗauki matakin ladabtarwa cikin gaugawa a kan duk jami’an da ke haɗa baki da wasu gwamnonin jihohi wajen bijire wa umarnin majalisar gudanarwa ta ƙasa.
Shugaban Majalisar Kwamared Joe Ajaero ya bayyana haka, a ƙarshen wani taron kwanaki biyu da su ka gudanar a gidan ƙwadago da ke Abuja, inda ya ce an cimma matsayar ne da nufin karfafa ƙungiyar NLC da kuma alakar masana’antu a Nijeriya.
Yayin da ya ke jawabi a ƙarshen taron, shugaban kungiyar ya shaida wa shugabannin zartarwa na jihohi cewa su zaɓi tsakanin ma’aikata ko su bar ofisoshin su.














































