Home Labaru Kasuwanci Nijeriya Ta Gargaɗi Bankuna A Kan Hulda Da Kamaru Da Vietnam Da...

Nijeriya Ta Gargaɗi Bankuna A Kan Hulda Da Kamaru Da Vietnam Da Croatia

395
0

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya bukaci bankunan kasuwanci
da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a Nijeriya su ƙara sa ido
wajen harkokin kasuwanci da mutane daga ƙasashen Kamaru
da Croatia da Vietnam.

Matakin dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare da hada-hadar kuɗi na bankin Mista Chibuzo Efobi ya fitar a Abuja.

Bankin CBN, ya ce bankunan Nijeriya da sauran cibiyoyin kudi akwai bukatar su yi hankali da yin hulɗar kasuwanci da waɗancan ƙasashe, saboda a baya-bayan nan Hukumar sa ido a kan ayyukan halasta kuɗin haram da kuɗaɗen aikata ta’addanci a duniya ta sa su a jerin ƙasashen da ake sanya wa idanu.

Sanarwar ta ce, an janyo hankalin bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi ga sakamakon da hukumar ta gudanar daga ranar 21 zuwa 23 ga watan Yuni na shekara ta 2023, inda ta sa Kamaru da Croatia da Vietnam a cikin jerin ƙasashen da za a ƙara sanya wa ido.

A watan Fabrairun da ya gabata, hukumar ta sanya Nijeriya a cikin jerin ƙasashen da za a sa wa ido, amma sanarwar baya- bayan nan daga Hukumar tattara bayanan sirri ta Nijeriya, ta ce yunkurin da Nijeriya ta yi na ficewa daga cikin jerin ya

LEAVE A REPLY