Hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa NERC, ta haramta wa
ma’aikatan kamfanonin rarraba wutar lantarki na DisCos
karɓar kuɗaɗe daga hannun mutanen da aka yanke ma wuta
saboda rashin biyan kuɗi.
Haramcin dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Sanusi Garba ya sanya wa hannu.
Sanarwar mai taken dokar kare mutuncin abokan hulda ta shekara ta 2023, ta ce za a riƙa karɓar kuɗaɗe ne daga hannun mutum yayin da aka maida ma shi wuta.
Sannan za a riƙa karɓar kuɗin bashin da ake bin sa a hankali kamar yadda mai amfani da wutar ya saba biya a baya, har zuwa lokacin da zai gama biyan duk abin da ake bin sa.
Dokar, ta kuma yi tsari a kan yadda za a riƙa karbar kuɗaɗen wuta daga hannun mutanen da ba su amfani da Mita wajen biyan kuɗin wutar, sannan ana sa ran za a rage yawan kuɗaɗen da ake karɓa daga hannun irin waɗannan mutane.
Wannan dai, ana ganin wani babban sauyi ne a kan tsarin karɓar kuɗaɗen wutar da ake yi a baya, inda ake ci-gaba lissafa wa mutum kuɗaɗen wuta duk kuwa da cewa an yanke ma shi wutar.