Home Labaru Labarun Ketare Neman Agaji: ‘Yan Nijeriya A Ukraine Su Na Cikin Tsaka-Mai-Wuya

Neman Agaji: ‘Yan Nijeriya A Ukraine Su Na Cikin Tsaka-Mai-Wuya

59
0
Wasu dalibai ‘yan Nijeriya da su ka makale a birnin Kherson na kasar Ukraine, sun bayyana mwuyacin halin da su ka fada bayan kwashe tsawon makonni biyu su na buya a wani daki da ke karkashin kasa.

Wasu dalibai ‘yan Nijeriya da su ka makale a birnin Kherson na kasar Ukraine, sun bayyana mwuyacin halin da su ka fada bayan kwashe tsawon makonni biyu su na buya a wani daki da ke karkashin kasa.

Daliban dai su na bukatar kasar su Nijeriya ta dauki matakin ceto su cikin gaugawa.

Jerry Kenny ya shaida wa manema labarai cewa, shi da wasu abokan sa 6 ba su da lafiya saboda mummunan halin da su ke cikin, inda ya ce ba su da abinci da sauran abubuwan more rayuwa.

Ya ce wasu daga cikin su ma ba su iya magana saboda fargaba, yayin da koka da cewa har yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta tuntube su ba da zummar sama masu ruwa da abinci.

Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama, ya ce ya tuntubi jakadun Nijeriya da ke Ukraine da Rasha, kuma sun tuntubi takwarorin su na Rasha da na Indiya domin samar da hanyoyin kwaso daliban daga Ukraine zuwa Nijeriya.