Home Labaru NDYC Ta Gargaɗi Matasan Neja-Delta Kan Tashin Hankali

NDYC Ta Gargaɗi Matasan Neja-Delta Kan Tashin Hankali

427
0

Ƙungiyar Matasan yankin Neja Delta NDYC, ta buƙaci
matasan su guji ayyukan da za su iya lalata zaman lafiyar da
ake samu a yankin.

Shugaban kungiyar na ƙasa Abido Jator ya yi wannan kiran a Abuja, yayin da ya ke roƙon matasan da ke ƙoƙarin tada hankali su janye zanga-zangar da su ke shirin yi na nuna adawa da hukumar raya yankin Neja Delta NDDC.

Abido Jator, ya ce ƙungiyar sa ta daƙile zanga-zangar da matasan su ka shirya a Unity Fountain da ke Abuja, ya na mai cewa al’ummar yankin Neja-Delta sun yi tashe-tashen hankula kuma yanzu su na buƙatar su koyi zaman lafiya.

Ya ce zaman lafiya wani ɓangare ne na ci-gaban zamantakewa da tattalin arziki, don haka a matsayin su na ‘yan ƙasa masu bin doka da oda, sun ga tashe-tashen hankula kuma smu na buƙatar su koyi bin hanyar zaman lafiya a yanzu.

LEAVE A REPLY