Gwamnatin tarayya ta kwaso ‘yan Najeriya 190 daga Haɗaɗɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), yayin da ƙasashen ke shirin gyara alaƙar difilomasiyya dake tsakanin su.
A cewar shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta Nema reshen yankin arewa ta tsakiya Bashir Garga,
wadanda aka kwason sun iso tashar jirgin sama na Nnamdi Azikiwe ne da misalin ƙarfe 5:57 na yau Talata.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana cikakken dalilin da ya sa aka kwaso su ba,
amma akan yi hakan ne akasari idan ‘yan ƙasa suka samu matsalar da ta sa ba za su iya cigaba da zama a ƙasar da suke ba.
Komowar tasu na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya da sanarwar da gwamnatin Najeriya ta bayar cewa ita da UAE sun cimma yarjejeniyar,
da za ta kai ga ɗage haramcin ba ‘yan Najeriya bizar shiga Dubai babban birnin UAE bayan sama da shekara ɗaya da hana su.
A shekarar da ta gabata, Najeriya ta kwashe jimillar ‘yan ƙasar ta 542 daga ƙasar da ke yankin Larabawa na Gabas ta Tsakiya.