Gwamnatin Najeriya ta ce ta cimma matsaya da hukumomin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wato DUBAI domin ci gaba da harkokin zirga-zirga tsakanin ƙasashen biyu.
A cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya fitar, ya ce bayan nasarar da aka samu wajen tattaunawa an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa,
wadda za ta ba masu riƙe da takardar tafiya ta fasgo na Najeriya samun izinin yin tafiya zuwa Haɗaɗɗiyar Daular ta Larabawa.
Sanarwar ta bayyana cewa yarjejeniyar ta fara aiki ne daga jiya 15 ga watan Yulin 2024,
wanda ke nufin cewa daga yanzu ƴan Najeriya za su iya ci gaba da zirga-zirga zuwa birnin Dubai na ƙasar ta UAE.
Wannan na zuwa ne sama da shekara biyu bayan da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ta dakatar da bayar da takardar biza ga ƴan Najeriya sanadiyyar ruɗani na diflomasiyya da ya shiga tsakani.
Kasar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabwa wato DUBAI na daga cikin ƙasashen da al’ummar Najeriya ke yawan ziyar ta,
ko dai domin kasuwanci ko kuma shaƙatawa.














































