Hukumar ta bayyana cewa jami’an hukumar ICPC ba su kai wa hukumar samame ba kamar yadda aka rika yaɗawa.
Fatima Sanda, mataimakiyar darektan yaɗa labarai na hukumar,
ta ce jami’an ICPC sun ziyarci hukumar ne domin gudanar da aiki kamar yadda suka saba a lokaci-lokaci.
Fatima Sanda, ta ce ba a kai wa NAHCON samame ba kamar yadda aka rika bugawa a wasu jaridu.
Jami’an ICPC sun ziyarci hukumar ne domin aiki kamar yadda suka saba lokaci-lokaci.
Sannan kuma babu wani ma’aikacin su da aka kama,
an dai gayyace wani babban ma’aikaci da suka tafi tare domin yi musu bayani kan wasu abubuwa da ya shige musu duhu
kuma ma da kansa ya bi su, sannan bayan ɗan ƙanƙanin lokaci ya dawo, ya ci gaba da aikin sa.
Sanda ta kara da cewa irin haka abu ne da hukumomi irinsu ICPC, EFCC ke yi a lokaci zuwa lokaci ga hukumomin gwamnati.
A ƙarshe ta hori kafafen yaɗa labarai su rika tantance lamari kafin su yaɗa domin gujewa faɗin abin da ba haka ba.














































