Home Labarai Na Bi Tsarin Mulki Wajen Yi Wa Joshua Dariye Da Jolly Nyame...

Na Bi Tsarin Mulki Wajen Yi Wa Joshua Dariye Da Jolly Nyame Afuwa – Buhari

25
0

Fadar shugaban kasa ta kare matakin ta na yi wa Joshua Dariye da Jolly Nyame, wadanda ke tsare a gidan yari saboda cin hanci da rashawa afuwa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Garba
Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya yi wa tsofaffin gwamnonin
afuwa ne saboda matsalar rashin lafiya bayan an duba yanayin
da su ke ciki.

Ya ce shawarar da majalisar magabata ta bada na a yi wa
tsofaffin gwamnonin da wasu mutane 157 afuwa, hukunci ne da
aka yanke cikin nutsuwa, kuma doka ta amince da hakan ba don
cimma wata manufar siyasa ba.

‘Yan Nijeriya da dama dai sun yi ta Allah-wadai da wannan
mataki, musamman duba da yadda masu fama da rashin lafiya
da ke zaune a gidan yarin ba a yi masu afuwa ba sai wadannan,
yayin da wasu ke korafi a kan wadanda su ka shafe shekaru a
gidan yari ba tare da an yi masu shari’a ba.

Garba Shehu, ya ce idan Buhari bai yi wa tsofaffin gwamnonin
afuwa ba za a rika yi ma shi kallon mutum maras tausayi.