Home Labaru N.U.E.E Ta Bukaci Ministan Lantarki Ya Yi Murabus Daga Kujerar Sa

N.U.E.E Ta Bukaci Ministan Lantarki Ya Yi Murabus Daga Kujerar Sa

910
0
N.U.E.E Ta Bukaci Ministan Lantarki Ya Yi Murabus Daga Kujerar Sa
N.U.E.E Ta Bukaci Ministan Lantarki Ya Yi Murabus Daga Kujerar Sa

Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Nijeriya N.U.E.E ta yi kira ga ministan lantarki Mamman Saleh da ya gaggauta yin murabus daga mukamin sa.

Kiran ya zuwa ne jim kadan biyo bayan gwamnatin tarayya tsige shugaban kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya Usman Muhammad a ranar Talata,19 ga watan Mayu.

Kungiyar N.U.E.E ta bukaci Mamman Saleh ya sauka daga mukamin sa ne saboda karancin ilimin kula da ma’aikatar da ya ke jogoranta.

Idan dai ba a manta ba, shugaban kasa Buhari ya sallami darakta na kamfanin raba wutar lantatrki T.C.N tare da ya maye gurbin sa da Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz a matsayin mukaddashi.

Leave a Reply