Home Home Mutum 150 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Kwara’

Mutum 150 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Kwara’

115
0

Ana ci-gaba da aikin nemo gawarwakin sauran mutane da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a jihar Kwara.

Rahotanni sun ce jirgin ya kife ne yayin da ya ke ɗauke da akalla mutane 300 da su ka fito daga wajen wani biki.

Wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin jihar Kwara dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnanm ta ce jirgin ya na ɗauke da mutanen da su ka fito daga garin Egboti na jihar Neja, a kan hanyar su ta zuwa Ƙaramar Hukumar Patigi ta jihar Kwara.

Sanarwar ta ce, mutanen da lamarin ya rutsa da su ‘yan asalin garuruwan Ebu da Dzakan da Kpada da Kuchalu da kuma Sampi ne duk a ƙaramar hukumar Patigi. Yayin zantawa da manema labarai, Sarkin Patigi ya ce bayanan da su ka samu sun nuna cewa, kimanin mutane 150 ne su ka rasa rayukan su, inda aka samu nasarar ceto mutane 53

Leave a Reply