Home Labaru Mutane Da Dama Sun Kone A Hatsarin Tankar Mai A Hanyar Abuja

Mutane Da Dama Sun Kone A Hatsarin Tankar Mai A Hanyar Abuja

1
0

Ana fargabar mutane da dama sun kone kurmus, sakamakon
gobarar da ta tashi bayan wata babbar mota dauke da mai ta yi
hatsari a hanyar Lakwaja zuwa Abuja.

Shaidu sun shaida wa manema labarai cewa, hatsarin ya faru ne bayan tankar da ke dauke da man ta kwace wa direban ta, inda ta yi taho-mu-gama da wata mota.

Wani ganau mai suna Yusuf ya shaida wa manema labarai cewa, tankar man da sauran motocin da abin ya rutsa da su su na kan ci da wuta, ciki har da wasu motocin Bas na haya da wata karamar mota.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen Jihar Kogi Stephen Dawlung ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an su sun isa wurin domin shawo kan lamarin.