Home Labaru Mukami: Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Nade-Nade

Mukami: Shugaba Buhari Ya Yi Sabbin Nade-Nade

154
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Abdulmumini Jibril, da  Gbenga Bareehu Ashafa, mukamin manyan daraktoci a hukumar kula da gidaje na gwamnatin tarayya FHA.

Hadimin gwamnan jihar Legas, Gawat Jubril, ne ya bada sanarwar nada Gbenga Bareehu Ashafa, a matsayin shugaban hukumar sai Abdulmumini Jibril a matsayin babban darakta.

Gawat Jubril, wanda ya ke taimakawa gwamna Babajide Sanwo Olu, a kan kafafen sadarwa na zamani ya bayyana wannan ne a shafin sa na Twitter.

Da ya ke bada sanawar Gawat Jubril ya ce Gbenga Ashafa, da Abdulmumini Jibril, za su fara aiki ne nan take.

Gbenga Ashafa, mai shekaru 65 ya wakilci mazabar sa a majalisar dattawa sau biyu daga 2011 zuwa 2019 a karkashin jam’iyyar ACN da APC.