Sama da mayaƙa 400 da suke addabar yankunan arewacin jamhuriyar Nijar ne suka miƙa wuya a birnin Agadez, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar, ANP ya ruwaito.
Rahoton ya ƙara da cewa mayaƙan dai duk ƴan ƙungiyar Patriotic Liberation Front de Movement for Justice and Rehabilitation of Niger ne.
Ya ce mayaƙan sun mika wuya ne sakamakon amincewa da kiran shugaban ƙasar Janar Abdourahmane Tchiani na miƙa wuya ne.
Ya ci gaba da cewa ba a taɓa samun mayaƙa da suka kai wannan adadin ba, sannan a ranar 3 da 11 ga watan Nuwamba ma an samu irin hakan, inda wasu mayaƙan daban suka miƙa wuya a birnin na Agadez.
Mayaƙan suna faɗa ne tare da kira a saki shugaban ƙasa Mohamed Bazoum da aka hamɓarar.