Kungiyar ISWAP ta yi awon gaba da akalla manoma shida a kauyukan da ke kusa da garin Mafa da ke Jihar Borno
Wani jami’in leken asiri, ya shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Tafkin Chadi, cewa akasarin wadanda harin ya rutsa da su ’yan gudun hijira ne.
Ya bayyana cewa mutanen sun bace ne bayan sun je gonarsu a kauyen Bulagarji, da ke kusa garin na Mafa.
’Yan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su, sun ce ’yan ta’addan sun far wa manoman ne da sanyin safiya inda suka kai su wani wuri da ba a sani ba.
Daya daga cikin ’yan uwan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ISWAP na neman kudin fansa Naira miliyan biyar kafin su sako wadanda abin ya shafa.
A wata mai kama da haka wasu masu garkuwa da mutane sun kashe wani Malam Muhammad, mazaunin bayan Jami’ar Maiduguri ranar Asabar 13 ga watan Agusta 2022.
Wani dan uwansa da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce masu garkuwa da mutanen sun kira iyalansa suka bukaci a ba su kudi Naira miliyan biyar amma iyalansa suka ce ba za su iya tara kudin ba saboda Naira miliyan uku ne kawai za su iya tarawa.