Home Labarai Matawalle Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Zaƙulo Makisan Sarkin Gobir

Matawalle Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Zaƙulo Makisan Sarkin Gobir

345
0
Bello Matawalle (1)
Bello Matawalle (1)

Ƙaramin ministan tsaro, ya sha alwashin za a zaƙulo tare da hukunta duk masu hannu a kisan Sarkin Gobirda ke jihar Sokoto, Isa Bawa.

A ranar Laraba ne labarin kisan sarkin ya fito bayan ya kwashe sama da mako uku a hannun ƴan bindiga.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktar ƴaɗa labaru ta ofishin ministan, Henshaw Ogubike, Matawalle ya yi tir da kisan sarkin,

tare da bayyana hakan a matsayin aikin rashin imani kuma abin da ba za a amince da shi ba.

Ya ƙara da cewa za a yi iyakar bakin ƙoƙari domin ganin an hukunta waɗanda ke da laifi a lamarin.

Takardar ta ce Matawalle ya umarci babban hafsan tsaron Najeriya ya ƙaddamar da bincike kan kisan nan take tare da tabbatar da ganin an hukunta duk wadanda ke da hannu cikin lamarin.

Leave a Reply