Home Labaru Ilimi Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima Za Su Fara Zuwa Bankuna Da...

Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima Za Su Fara Zuwa Bankuna Da Sauran Masana’antu

43
0
nysc 1
nysc 1

Gwamnatin tarayya ta dage takunkumin da ta kakaba wa masu yi wa kasa hidima (NYSC) zuwa masana’antu masu zaman kan su, wanda hakan zai ba masu hidimar damar yin aiki a masana’antu kamar su banki da masana’antun mai da iskar gas.

Wannan sabon sauyin, wanda Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande ya sanar, zai fara aiki ne akan masu yi wa kasa hidiman bangaren Batch ‘C’ na shekarar 2024.

Wannan sabon tsarin, ya soke wani tsari ne da ya takure masu yi wa kasa hidiman a bangaren fannin ilimi, da noma, da lafiya, da ababen more rayuwa kawai.

Wannan tsarin, wanda aka bullo da shi a lokacin tsohon Ministan Matasa, Bolaji Abdullahi, ya yi kokarin kiyaye darajar masu yi wa kasa  hidima domin hana kamfanonin masu zaman kan su wulakanta su.

Sai dai, wannan sabon tsarin zai fara aiki ne a Legas da Abuja, inda za a tura masu yi wa kasa hidima zuwa masana’antu masu zaman kan su da suka hada da zababbun bankuna da kamfanonin mai da iskar gas.

Leave a Reply