Home Labaru Matar Tinubu Ta Kai Wa Aisha Buhari Ziyara Fadar Shugaban Ƙasa

Matar Tinubu Ta Kai Wa Aisha Buhari Ziyara Fadar Shugaban Ƙasa

345
0

Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari, ta zagaya da matar
zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinubu domin nuna
mata lungu da saƙon gidan da shugaban ƙasar ke zama tare da
iyalan sa.

A’isha Buhari, ta ce gidan da a yanzu iyalan shugaban ƙasa ke zaune a ciki da ake kira ‘Glass House’ a Turance, shi ne gidan da shugaban ƙasa mai barin gado da iyalan sa za su zauna gabanin sauka daga mulki.

Ta ce gidan shi ne muhallin da shugaban ƙasa mai barin gado zai koma domin bada damar yi wa ainihin gidan shugaban ƙasa mai jiran-gado kwaskwarima.

Sanata Oluremi Tinubu ta yaba wa A’isha Buhari bisa tarbar da ta yi mata, inda ta alƙawarta yin aiki tuƙuru domin ci- gaban al’ummar Nijeriya.

Leave a Reply