Home Labarai Matakin Gaggawa: Majalisa Ta Bukaci Hukumomin Tsaro Su Magance Hare-Haren ‘Yan Ta’Adda

Matakin Gaggawa: Majalisa Ta Bukaci Hukumomin Tsaro Su Magance Hare-Haren ‘Yan Ta’Adda

97
0

Majalisar dattawa ta koka kan tabarbarewar harkar tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya, ta kuma bayyana cewa, za ta kakkabe rahottani da ta yi tun shekara 2015 domin ta kai wa shugaban kasa saboda a dauki matakin gaggawa.

Matakin da Majalisar dattawan ta dauka ya biyo bayan wani kuduri ne da sanata Emmanuel Udende ya gabatar a zauren Majalisar inda ya koka cewa an kashe mutane sama da 50 a wasu sabbin hare haren da yan ta’adda suka kai a wasu kauyukan jihar Binuwai da suka hada da Kwande, da Ukum, da Logo, da Katsina Ala.

Majalisar ta bukaci shugabanin hukumomin tsaro su gaggauta tura jami’an tsaro domin magance cigaba da hare haren da ‘yan ta’adda masu dauke da makamai su ke kwaiwa a fadin kasa.

A bayanin sa, Sanata Adamu Aliero ya yi nazari cewa, Majalisar na da rahottani da shawarwari tun daga shekara 2015 inda ya ce kullum ana kawo masu rahoton kashe mutane ana tagayyara su, ana kuma kona garuruwa, da hana mutane shiga gonakin su domin su yi noma saboda a samu abinci.

Aliero ya ce yanzu shugabanin Majalisar za su kai wadannan rahottanin ga Shugaban kasa kuma suna so a aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahottanin.

Leave a Reply