Majalisar Masarautar Zazzau, ta dakatar da Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah daga kujerar sa ta Marafan Yamman Zazzau, biyo bayan koken da al’ummar Unguwar Magajiya da ke birnin Zariya su ka gabatar na zargin cin zarafin wani mutum da ake yi wa basaraken.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta Abdullahi Aliyu Ƙwarbai ya fitar, masarautar ta ce ta amince cikin gaugawa ta dakatar da Hakimin har sai abin da hali ya yi nan gaba.
Alhaji Mustapha dai majalisar ta same shi ne da laifin zartar da hukunci a kan wani Yusuf Yahaya mazaunin Unguwar Magajiya, wanda a bisa tsarin doka ba ya da hurumin ɗaukar irin wannan mataki.
Masarautar Zazau, ta kuma janyo hankalin dukkan Hakimai da Dagattai da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya cewa, ba za ta lamunci cin zarafi ko tozarta kowane irin jinsi na al’umma ba.
Alhaji Mustapha Ubaidullah, ya ce ya sa an bugi shi wanda ake zargin ne saboda ya kama shi ya na luwaɗi da wani yaro a bayan gidansa, sannan ya buƙaci a gabatar da shi ga hukuma maimakon dakatar da shi da aka yi ba tare da binciken abin da ya sa ya ɗauki wannan matakin ba.