Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce har gobe shi ne shugaban jam’iyyar APC duk da hukuncin da alƙalin babbar kotun jihar Kano ya zartar na cewa ya daina bayyana kan sa a matsayin dan jam’iyyar.
Tsohon gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje ya ce sun rubuta takardar koke kan alƙalin da ya tabbatar da dakatarwar da aka yi masa tare da sanar da jami’an tsaro cewa wanda ya bayar da sanarwar dakatar da shi sojan gona ne.
Ya shaida cewa abubuwan da suke faruwa abubuwa ne waɗanda dole sai an tashi sosai da sosai domin sabon shaƙiyanci ne yake nema ya shiga dimokraɗiyya a Najeriya musamman a jihar Kano.