Home Labaru Malami Ya Ce Shugaba Buhari Ya Ceto Najeriya Daga Durkushewa A 2015

Malami Ya Ce Shugaba Buhari Ya Ceto Najeriya Daga Durkushewa A 2015

309
0

Ministan Shari’a kuma babban Lauyan Gwamnati, mai mukamin SAN Abubakar Malami, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ceto Najeriya daga durkushewa cikin shekarar sa ta farko bayan karbar mulki a shekara 2015.

Abubakar Malami ya ce shugaba  Buhari ya ceto Najeriya ne yayin da take shirin rushewa sakamakon karyewar tattalin arziki da sauran matsaloli cikin kankanin lokaci.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin gidan Rediyon Kano, inda ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu mummunan koma baya kafin zuwan Buhari a shekarar 2015.

Ya ce abin da shugaba Buhari ya cimma cikin kankanin lokaci ko kasashen da suka ci gaba ba za su iya ba.

Abubakar Malami ya ce kafin zuwan shugaba Buhari, akwai matsalolin tsaro da yawa, musamman a Arewa maso Gabas, amma a yanzu an yi nasarar dakile hare-hare domin a yanzu a kan shafe tsawon lokaci kafin aji an kai hari Kasuwanni, ko wuraren ibada da dai sauran su.

Har wa yau, ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro ke aiki tukuru wajen ganin an kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a Arewa maso yamma.


RAHOTO- ABUJA

Leave a Reply