Home Labaru Majalisar Zartarwa: Gwamnatin Tarayya Zata Kashe Dala Biliyan 3 Domin Bunkasa Hukumar...

Majalisar Zartarwa: Gwamnatin Tarayya Zata Kashe Dala Biliyan 3 Domin Bunkasa Hukumar Kwastam

168
0

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta ba da lamunin fitar da Dala biliyan 3.1 domin karasa aikin inganta harkokin gudanarwa a Hukumar Hana Fasakwauri ta kasa.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Shamsuna Ahmed, ce ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan halartar zaman Majalisar Zartarwa da Shugaba Buhari ya jagoranta a fadarsa dake Abuja.

Ta ce makasudin hakan shi ne mayar da dukkan harkokin gudanarwar Hukumar Kwastam su koma amfani da fasahar sadarwar zamani.

A cewarta ministan, kudaden yarjejeniyar kwangilar aikin na tsawon shekara 20 za su fito ne daga masu zuba jari da kuma kudaden shiga da Hukumar zata samu.

A nasa jawabin Ministan yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta fitar ko sisi daga lalitarta ba yayin gudanar da aikin.