Home Home Majalisar Wakilan Najeriya Ta Nemi Ɓullo Da Shirin Rage Raɗaɗi Bayan Cire...

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Nemi Ɓullo Da Shirin Rage Raɗaɗi Bayan Cire Tallafin Mai

88
0

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin tarayya ta cika alƙawarin da ta ɗauka na samar da matakan daƙile illolin cire tallafin man fetur ga ‘yan Nijeriya.

Kiran dai ya na zuwa ne, bayan amincewa da wani kudurin da dan majalisa Aliyu Sani Madaki na jam’iyyar NNPP daga jihar Kano ya gabatar a zauren majalisar.

Da ya ke gabatar da kudurin, Aliyu Sani ya ce  a ranar 29 ga watan Mayu ne, shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, lamarin da ya sa farashin litar mai ya ƙaru daga Naira 194 zuwa sama da Naira 500 a gidajen mai.

Ya ce tun da ga lokacin ‘yan Nijeriya su ke fama da hauhawar farashin man fetur, da kuma illar da ke tattare da hakan musamman kayayyakin masarufi da su ka hada da abinci da ayyukan da duk farashin su ya tashi. Majalisar ta ɗora wa kwamitin ƙwadago alhakin yin nazari a kan lamarin, tare da bada rahoto domin ci-gaba da aiwatar da shawarwarin da aka bada

Leave a Reply