Home Home Majalisar wakilai ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamiti, domin gudanar...

Majalisar wakilai ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamiti, domin gudanar da bincike a kan yadda aka gudanar da aikin farfado da jirgin sama na kamfanin Nigerian Air.

77
0

Shugaban kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen sama na majalisar wakilai Nnolim Nnaji ya gabatar da bukatar a Abuja, bayan nazarin da ya kammala a kan lamurran da su ka shafi jirgin saman.

Kwamitin, ya kuma bukaci a gurfanar tare da hukunta duk jami’an da ke da hannu a shirin kaddamar da jirgin Nijeriya, wanda ya yi batan-dabo jim kadan bayan gabatar da shi, lamarin da ‘yan majalisar su ka bayyana a matsayin damfara.

Rahotanni sun ce, Kwamitin ya bayyana rashin gamsuwa da ayyukan tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ne, yayin sauraren bayanan wasu jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki da su ka bayyana a gaban sa domin bada bahasi a kan abin da su ke da masaniya a kai.

Mukaddashin babban manajan kamfanin jiragen sama na Nijeriya Kyaftin Dapo Olumide, ya ce babu shakka sun yi amfani da jirgin Ethiopian Air ne wajen gabatar da jirgin sama na Nigerian Air.

Leave a Reply