Majalisar Tattalin Arziki, ta shawarci Shugaba Bola Tinubu
ya saida kadarorin gwamnati a biya basussukan da ake bin
Nijeriya.
‘Yan majalisar, wadanda su ka hada da Tokunbo Abiru a matsayin shugaba, da Yemi Cardoso da Sumaila Zubairu da Doris Anete, sun shawarci Shugaba Tinubu cewa gwamnatin shi ta kafa tsari a kan yadda duk kuɗaɗen cinikin kadarorin da za a saida su tafi wajen biyan bashin da ake bin gwamnatin tarayya.
Sun kuma bada shawarar cewa a faɗaɗa kwangilar aikin samar da tsaro a Yankin Neja Delta, ta hanyar ƙara jam’ian tsaro sannan a ƙara yawan ɗanyen man da ake haƙowa a yankin.
Majalisar, ta kuma bada shawara a riƙa tace ganga miliyan 2 a kowace rana, tare da bada shawarar a gaggauta fara amfani da Gidauniyar Bunƙasa Yankin da ake Haƙo Ɗanyen Mai.














































