Home Labarai Majalisar Shura: Abba Ya Naɗa Manyan Malamai 46

Majalisar Shura: Abba Ya Naɗa Manyan Malamai 46

357
0
Abba Kabir Yusuf e1687267111500
Abba Kabir Yusuf e1687267111500

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya naɗa manyan malaman Musulunci 46 daga ɗariku daban-daban tare da ƙwararru daga fannoni daban-daban a matsayin majalisar ƙoli ta jihar Kano.

Gwamnan na jihar Kano ya kafa Majalisar Shurar ce mai ɗauke da manyan malaman Musulunci da ƙwararrun domin ba shi shawara kan al’amuran mulkin jihar.

Gwamnan ya ba babbae majalisar shawa ta jihar ne kasa da awa 24 bayan ya sallami Sakataren Gwamnati ya rushe ofishin shugaban ma’aikatan sa tare da sallamar kwamishinoni biyar.

Majalisar wadda za ta kasance ƙarƙashin jagorancin Farfesa Shehu Galadanci an kafa ta ne domin tafiya tare da kowane ɓangare da nufin ba wa gwamnan shawarwari ta fuskan addini da shugancin da sauran al’amuran da suka shafi al’ummar jihar.

Mataimakin Shugaban Majalisar Shura shin ne Farfesa Muhammad Sani Zahradeen.

Leave a Reply