Home Labaru Majalisar Kano Ta Tantance Kwamishinoni 17 A Cikin 19 Da Gwamna Ya...

Majalisar Kano Ta Tantance Kwamishinoni 17 A Cikin 19 Da Gwamna Ya Aike Mata

99
0

Majalisar Dokoki ta Jihar Kano, ta amince da mutane 17 daga cikin 19 da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin amincewa da su a matsayin kwamishinonin jihar.

Rahotanni sun ce, Majalisar ta amince da sunayen ne a bisa ƙarƙashin jagorancin kakakin ta Isam’il Falgore.

An dai amince da mutane 17 daga cikin 19 da gwamnan jihar ya aike wa majalisar, in ban da Sheikh Tijjani Auwal da Hajiya A’isha Soji, waɗanda ba su halarci majalisar ba sakamakon tafiyar su aikin Hajji.

Bayan kammala tantance kwamshinonin, yanzu kuma hankali ya koma a kan ma’aikatun da kwamshinonin za su jagoranta bayan an rantsar da su.

Leave a Reply