Makonni uku kenan da kammala hutun ƴan majalisar dokokin jihar Kano.
sai dai kuma komawa majalisar ya gagare su saboda fargabar tayar bama-bamai da ake zargin wasu za su yi a harabar zauren Majalisar,
Majiyoyi sun ce tsaikon da aka samu ya biyo bayan gargadin da ‘yan sandan suka yi na wani shiri da wasu batagari suka yi na tada bama-bamai a harabar majalisar.
A ranar 26 ga watan Mayu ne tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel,
ya ce jami’an tsaro sun samu rahoton sirri cewa wasu ƴan ta’adda na shirin tayar da bam a harabar majalisar.
Wasu na alakanta batun da rusa masarautu da gwamnatin Kano ta yi da tun
bayan haka ake ta kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Kano da hukuncin kotu game da rusa masarautun da kuma dawo da Sarki Sanusi kan karagar mulkin Kano.














































