Home Home Majalisar Dattawa Ta Yi Magana Kan Ministocin Da Tinubu Zai Naɗa

Majalisar Dattawa Ta Yi Magana Kan Ministocin Da Tinubu Zai Naɗa

211
0

Da yiwuwar majalisar dattawa ta ɗage shirin ta na tafiya hutun shekara, yayin da ake tsammanin isowar sunayen ministocin shugaban ƙasa domin tantancewa.

Sanatoci dai su na tsammanin shugaba Bola Ahmed Tinubu zai aika da sunayen ministocin ne a farkon mako mai zuwa.

Ɗaya daga cikin shugabannin majalisar dattawa, ya ce ana tsammanin Sanatoci za su tafi hutun su na shekara daga ranar 27 ga watan Yuli, 2023 zuwa watan Satumba, sai dai ya ce majalisar a shirye su ke su riƙa zama kowace rana domin tabbatar da sun tantance Ministocin da aka naɗa.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dattawa Sanata Yemi Adaramodu, ya ce majalisar ta na da isasshen lokacin duba buƙatar shugaban kasa kafin tafiya hutu.

Ya ce har yanzu ba a sanar da ranar tafiya hutun shekara ba a majalisar dattawa, don haka tambaya a kan yiwuwar ɗaga lokacin ba ta taso ba kwata-kwata.

Leave a Reply