Majalisar Dattawa ta yi kira ga Babban Bankin Nijeriya ya ƙara wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun Naira zuwa ranar 30 ga watan Yuni na shekara ta 2023.
Idan dai ba a manta ba, a watan da ya gabata ne Bankin CBN ya gabatar da sababbin takardun kuɗin da aka sauya fasali, wadanda za su fara zagawa a hannun jama’a da bankuna daga ranar 15 ga watan Disamba na shekara ta 2022, zuwa ranar 31 ga watan Janairun shekara ta 2023.
A wani ƙuduri da Sanata Ali Ndume ya gabatar, ya nemi babban bankin ya ɗage wa’adin daina karbar tsofaffin takardun Naira zuwa watan Yuni na shekara ta 2023.
Sanata Ndume, ya ce tun farko tsarin sauya fasalin kuɗin bai tafi yadda ya kamata ba, domin har yau sababbin kuɗin ba su fara Zagawa a tsakanin al’ummar birane ba balle a yi maganar mutanen karkara.
Ndume ya kara da cewa, ya na sane da cewa tun a ranar 15 ga watan Disamba bankuna su ka bude damar masu ajiyar kudi su je su canza kuɗaɗen su zuwa sababbi kafin zuwa ranar 31 ga watan Janairu na shekara ta 2023.














































