Home Home Ina Goyon Bayan Takarar Binani A Jihar Adamawa – Buhari

Ina Goyon Bayan Takarar Binani A Jihar Adamawa – Buhari

121
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zaben Sanata A’isha Dahiru Ahmed Binani a matsayin Gwamnan Jihar Adamawa zai bude sabon babi da ga ‘yan’uwan ta mata a fadin Nijeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zaben Sanata A’isha Dahiru Ahmed Binani a matsayin Gwamnan Jihar Adamawa zai bude sabon babi da ga ‘yan’uwan ta mata a fadin Nijeriya.

Buhari ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a ba mata gurabe su fito a dama da su a bangaren gudanar da shugabanci a Nijeriya.

Da ya ke jawabi a fadar Lamidon Adamawa a garin Yola, Shugaba Buhari ya ce zai taimaka wa takarar Binani dari bisa dari, kuma zai cigaba da ba ta kwarin gwiwa a kan wannan mataki na neman gwamna da ta ke yi.

A nasa jawabin, gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya gode wa shugaba Muhammadu Buhari bisa ayyukan da ya shimfida a jihar daban-daban.

Lamidon Adamawa Alhaji Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, ya yaba wa shugaba Buhari bisa mukaman da ya ba ‘yan asalin jihar Adamawa a gwamnatin sa, wadanda su ka hada da na ministan birnin tarayya Abuja Mohammed Musa Bello, da sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da kuma shugaban hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya Janar Buba Marwa.

Leave a Reply