Home Labaru Kasuwanci Majalisa Za Ta Ƙayyade Jarin Naira Biliyan 500 Ga Kamfanonin Rarraba Lantarki

Majalisa Za Ta Ƙayyade Jarin Naira Biliyan 500 Ga Kamfanonin Rarraba Lantarki

33
0
PHCN SUBSTATION AT MAKERI
PHCN SUBSTATION AT MAKERI

Majalisar wakilai ta bayar da shawarar ƙayyade naira biliyan ɗari biyar, a matsayin jari mafi ƙankanta da kamfanoni goma sha ɗaya da ke rarraba wutar lantarki na ƙasa, wato DisCos, za su mallaka,

Hakan ya biyo bayan damuwar da ake ta nunawa, cewa kamfanonin rarraba lantarkin suna fama da ƙarancin kuɗin aiwatar da ayyukan su yadda kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, har a ci ribar da ta kamata.

Ƴan majalisar wakilan Najeriyar suna ganin matuƙar ba ƙara yawan jarin kamfanonin raba wutar lantarkin aka yi ba, to ba za su iya ci gaba da gudanar da ayyukan su yadda ya kamata ba.

Asali ma dai za su yi ta zama wata babbar barazana ce kawai ga ci gaban tattalin arziki Najeriya da jin daɗin jama’ar ƙasa.

Saboda haka, majalisar ta ƙarfafa cewa, wajibi ne kamfanonin raba wutar lantarkin na Najeriya su ƙara jarin su da aƙalla naira biliyan ɗari biyar ba.

Leave a Reply