Jami’ar Abuja ta sanar da fatattakar dalibai 100 bisa rashin bin ka’idar jarrabawa, inda ta ce wadanda aka kora sun hada da masu karatun matakin digiri 72, da masu karatun digiri na biyu su 28.
Kakakin jami’ar Habib Yakub, ya ce an kuma dakatar da wasu dalibai biyar da ke karatun digiri na tsawon zangon karatu guda.
Ya ce an kuma dakatar da wasu mutane uku da ke karatun digiri na biyu tsawon zangon karatu guda, kuma majalisar zartarwa ta jami’ar ta amince da korar daliban.
Habib Yakub ya kara da cewa, an umurci daliban da lamarin ya shafa su mika duk wasu kaya mallakin jami’ar, ciki kuwa har da katin shaidar su zuwa ga Shugaban sashen su.
Ya
ce an kuma shawarci daliban su yi gaugawan barin makarantar, sannan duk dalibin
da ya saba tsarin makarantar zai fuskanci hukuncin da ya dace da shi.