Home Labaru Kiwon Lafiya Mafi Yawan Masu Dauke Da Nau’In Omicron Na Afrika – WHO

Mafi Yawan Masu Dauke Da Nau’In Omicron Na Afrika – WHO

108
0

Hukumar Lafiya ta Duniya tace kashi 46 na masu ɗauke da sabon nau’in korona ta Omicron sun fito ne daga Kasashen Afrika 10.

Ta ce yawancin ƙasashen na kudancin Afrika, kamar yadda alƙalumma na cikin gida suka nuna, inda masana ke ƙara sa ido kan ƙaruwar masu kamuwa da cutar da kuma bincike kan samfurinta domin gano sauye-sauyentata.

Sai dai masu kwanciya asibiti da kuma waɗanda cutar ta yi wa muni har yanzu ba su da yawa, kamar yadda alƙalumma na cikin gida suka nun amma har yanzu ana ci gaba da bincike, a cewar WHO.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa hana shigar baƙi ba zai hana bazuwar cutar ba, amma rigakafi zai yi tasiri ga rage bazuwarta.