Home Labaru Mabiya Kwankwasiyya Sun Yi Wa Pantami Ihu A Kano

Mabiya Kwankwasiyya Sun Yi Wa Pantami Ihu A Kano

765
0

Wani bidiyo da ya karade kafafen sadarwar zamani, ya na dauke da yadda wasu mabiya darikar Kwankwasiyya suka ci mutuncin fitaccen Malamin addinin Islama kuma Ministan Sadarwa Isah Ali Pantami.

A cikin bidiyon dai, ana iya ganin Pantami da jami’an tsaro da kuma yaran Kwankwasiyya, inda ‘yan Kwankwasiyyan su ke yi wa Malamin ihun ‘Ba ma yi’, yayin da wasu ke kokarin cafko shi, amma jami’an tsaro su ka yi ta kokarin kare shi.

Lamarin dai, ya faru ne a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano, a daidai lokacin da Ministan ya ke kan hanyar sa ta komawa Abuja ranar Talatar da ta gabata.

Sai dai abin da mabiya Kwankwasiyyar su ka yi ya janyo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke ganin hakan bai kamata ba, duba da cewa baya ga kasancewar sa minista, Isah Ali Pantami Malamin addini ne da ya ke amfanar da al’umma.