Home Labarai Ma’aikata A Zamfara Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

Ma’aikata A Zamfara Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

240
0
nlc zamfara.jpg4
nlc zamfara.jpg4

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC rehen jihar Zamfara ta sanar da shirin ma’aikatan jihar na tsunduma yajin aiki nan da ƙarshen wannan wata na Nuwamba, muddin gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon albashi mafi ƙaranci ba.

Ƙungiyar ta ce matakin jan ƙafar na nuna yadda wasu gwamnonin jihohi ba su jin tausayin ma’aikata musamman a wannan lokaci da al’umma ke fama da tsadar rayuwa.

Gwamnatin Zamfara dai ta sanar da amincewa da naira dubu 70 ne a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar.

Leave a Reply