Ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya reshen Jihar Nasarawa, ta fara
yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar bayan gwamnati ta gaza
wajen cimma buƙatun ‘ya’yan ta.
Shugaban kungiyar na jihar Mista Peter Attah ya bayyana wa manema labarai haka a garin Lafia, inda ya ce sun yanke shawarar tafiya yajin aikin ne a wajen wani taro da ƙungiyar ta shirya.
Mista Peter Attah, ya ce gwamnati ta gaza wajen cimma buƙatun su a cikin wa’adin kwanaki 21 da ƙungiyar ta ƙayyade mata daga ranar 13 ga watan Yuni na shekara ta 2023.
Ya ce daga cikin dalilan da su ka haifar da yajin aikin akwai batun rashin ƙarin girma ga likitoci, da rashin ƙarin albashi na shekara-shekara da rashin biyan mafi ƙarancin albashi da dai sauran su.














































