Home Labaru Lauyan Atiku Ba Ya Da Lasisin Shiga Harkokin Shari’a A Najeriya –...

Lauyan Atiku Ba Ya Da Lasisin Shiga Harkokin Shari’a A Najeriya – INEC

398
0
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce korafin da Atiku Abubakar ya gabatar a gaban kotun bai samu sa hannun Lauya mai lasisin shiga harkokin shari’a a Nijeriya ba.

Atiku Abubakar dai ya shigar da korafi a gaban kotun daukaka kara, domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019.

Yanzu haka dai kimanin lauyoyi 32 ke wakiltar Atiku Abubakar a kotu, a karkashin jagorancin babban Lauya Livy Uzoukwu.Sai dai hukumar zabe ta ce, Lauyan Atiku ba ya da cancantar shiga al’amuran shari’a a Nijeriya, sakamakon rashin samun lasisin wakilcin shari’a daga kotun koli ta Nijeriya.

Leave a Reply