Home Labaru Labaran Ƙarya Na Barazana Ga ‘Yancin Faɗin Albarkacin Baki – Ahmed Maiyaki

Labaran Ƙarya Na Barazana Ga ‘Yancin Faɗin Albarkacin Baki – Ahmed Maiyaki

470
0

Babban Jami’in Yaɗa Labarai na Ci-gaban Ƙungiyar
Fafutukar Neman ‘Yancin ‘Yan Jarida Malam Ahmed
Maiyaki, ya bayyana damuwa a kan ƙalubalen da ake fuskanta
na ‘yancin aikin jarida a Nijeriya.

Ahmed Maiyaki, ya bayyana labarun ƙarya a matsayin wani ɓangare da ke barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki a matsayin kan gaba ga sauran ‘yancin ɗan adam.

Ya ce ko da ya ke matsayin ‘yan jarida na duniya ya na da muhimmanci wajen samar da manufofin dimokuraɗiyya da ‘yancin yada labarai, amma labarun ƙarya sun zama babbar barazana ga ‘yancin faɗin albarkacin baki da aikin yaɗa labarai da dimokraɗiyya mai ɗorewa.

Ahmed Maiyaki, ya kuma gargaɗi masu aikin yaɗa labarai su yi taka-tsan-tsan da madogarar su ta hanyar tantance gaskiya domin tabbatar da sahihanci da kauce wa rikice-rikice.

Ya ce dole ne ‘yan jarida su kasance masu bin doka da kuma kare muradun al’umma, ta hanyar tattara sahihan bayanai da yaɗa labarum da ke tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY