Rahotanni daga jihohi da dama sun nuna cewa, akalla
Kwamishinoni 53 da ma’aikatan gwamnoni da dama ne su ka
ajiye aikin domin tsayawa takara a zaben shekara ta 2023.
Hakan kuwa ya faru ne, bayan wasu gwamnoni sun bukaci su
sauka daga mukaman su domin yin biyayya ga dokokin zabe da
ya umarci masu sha’awar su yi murabus.
Wannan ya na zuwa ne, a daidai lokacin da ministocin da ake
ganin su na son tsayawa takara ke ci-gaba da zama a kan
mukaman su.
Daga cikin su kuwa akwai Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, da
Ministan Kwadago Chris Ngige da Ministan Shari’a Abubakar
Malami, da sauran masu rike da manyan mukamai a hukumomin
gwamnati.
Rahotanni sun nuna cewa, Kwamishinoni da masu bada shawara
akalla 12 ne su ka mika wa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq
na Jihar Kwara takardun yin murabus.
A jihar Kano, bayanai sun ce akalla Kwamishinoni 10 ne su ka
ajiye aiki, ciki kuwa har da Mataimakin Gwamna Nasir
Gawuna, wanda shi ne Kwamishinan Noma.