Kungiyar likitoci ta Nijeriya reshen jihar Nasarawa ta dakatar
da yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar, inda ta ba gwamnatin
jihar wa’adin makonni biyu ta biya masu dukkan bukatun su.
Idan dai ba a manta ba, kungiyar ta shiga yajin aikin ne bayan gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da ƙarin matsayi ga wasu ‘ya’yan ta har na tsawon shekaru tara da ƙarin albashi sama da shekaru 12.
Da ya ke zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan wani taron gaugawa a Lafia, shugaban kungiyar Dakta Peter Attah, ya ce sun yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne domin rage wahalhalun da al’ummar jihar su ka shiga.
Dakta Peter Attah, ya ce kungiyar ta umarci ‘ya’yan ta su koma bakin aiki cikin gaugawa domin ceton rayuka.














































