Wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne dauke da makamai a cikin motoci da Babura, sun kai hari wuraren
binciken jami’an tsaron rundunar hadin gwiwa ta Operation
Hadin Kai da ke yankin Molai a jihar Borno.
Wani shaidun gani da ido ya shaida wa manema labarai cewa,
bayan kazamin artabu, an kashe jami’in soji daya, yayin da wani
ya samu Rauni.
Wata majiya ta ce, ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da wata
motar yaki ta soji da motar daukar marasa lafiya kafin su tsere
bayan isar jiragen sama na yaki .
Bayanai sun ce, lamarin ya sa mazauna kauyukan Lawanti Kura
da NNPC Depot da Molai tserewa domin tsira da rayukan su.














































