Home Labaru Kuma Dai: ‘Yan Bindiga Sun Sace Wata Mai Taimakon Talakawa Da ‘Yar...

Kuma Dai: ‘Yan Bindiga Sun Sace Wata Mai Taimakon Talakawa Da ‘Yar Ta a Kaduna

380
0

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mai aikin taimakon jama’a Ramatu Abarshi da ‘yar ta Amira, bayan sun gama raba kayan sallah ga al’ummar garin Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun afka ma su ne kusa da Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kachia.

Ramatu Abarshi, wadda tsohuwar shugabar sashen Injiniyan Lantarki na kwalejin jihar Kaduna ce, ta yi suna sosai wajen aikin taimakon jama’a da shirin zaman lafiya a kudancin Kaduna.

Wata majiya ta kusa da iyalan ta ce, ‘yan bindigar sun tuntubi iyalan matar, inda su ka bukaci a biya naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar su.

Leave a Reply