Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa’i, ya kalubalanci tsofaffin gwamnonin jihar Kaduna su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su saci dukiyar talakawa a lokacin da su ke kan mulki ba.
El-rufa’i ya kalubalanci tsofaffin gwamnonin ne, a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta KSMC kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce daya daga cikin tsofaffin gwamnonin ya ma gina wani katafaren gida a kan titin Jabi da ke unguwar masu hannu da shuni a Kaduna da kudin talakawan jihar.
Gwamna El-Rufa’i ya kara da cewa, idan ba tsoro ba gwamnonin da su ka shude su fuskanci al’ummar jihar Kaduna su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su taba sata daga asusun gwamnati ba.
Gwamnan ya ce bai taba satar kudin talakawa ba tun da ya zama gwamnan jihar Kaduna, kuma zai iya rantsewa da Allah a kan haka.
You must log in to post a comment.