Home Labaru Kotun Ƙolin Najeriya Ta Bai Wa Ahmad Lawan Takarar Sanatan Yobe Ta...

Kotun Ƙolin Najeriya Ta Bai Wa Ahmad Lawan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa

129
0

Kotun Koli ta tabbatar da Sanata Ahmad Lawan a matsayin halastaccen ɗan takarar kujerar sanata na mazabar Yobe ta arewa.

Da ya ke yanke hukuncin, alƙalin kotun mai shari’a Centus Nweze, ya ce Bashir Machina ya gaza gabatar wa babbar kotun tarayya da ke Damaturu hujjar zargin aikata maguɗi a zaɓen fidda gwani.

Jam’iyyar APC ce ta ƙalubalanci Bashir Machina a matsayin ɗan takarar ta na kujerar sanatan, ta na mai cewa Ahmad Lawan ta sani a matsayin halastaccen ɗan takara.

A zaman sauraron ƙarar da ya gabata, lauyan jam’iyyar APC Sepiribo Peters, ya ce zaɓen fitar da gwanin da ya ba machina nasara ya saɓa wa dokar zaɓe ta shekara ta 2022, domin ba jam’iyyar ce ta naɗa Danjuma Manga a matsayin jami’in da ya jagoranci zaɓen fidda gwanin ba.

Sanata Ahmad lawan dai bai shiga takarar fidda gwani na farko da jam’iyyar APC ta gudanar ba, kasancewar ya shiga takarar kujerar shugaban ƙasa.

Leave a Reply