Home Labaru Kotu Ta Yanke Wa Ɗan Abdulrasheed Maina Hukuncin Shekara 24 A Gidan...

Kotu Ta Yanke Wa Ɗan Abdulrasheed Maina Hukuncin Shekara 24 A Gidan Yari

18
0
Faisal Maina

Wata babbar kotun tarayya dake babban birnin tarayya Abuja ta yanke wa ɗan tsohon shugaban hukumar fansho Faisal Abdulrasheed Maina, hukuncin ɗaurin shekara 24 a gidan yari.

A yayin yanke hukuncin a ranar Alhamis din nan, Mai Shari’a Okon Abang ya samu Faisal da laifuka uku da suka haɗa da halatta kuɗin haram, wanda hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta tuhume shi da su.

Mai Shari’a Abang ya ce EFCC ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Faisal ya yi amfani da wani asusun ajiya na bankin  UBA, inda mahaifinsa ya yi zambar kudi Naira Miliyan 58.1.

Kotun ta ce an tura kuɗin ne asusun mai ɗauke da sunan Alhaji Faisal Farm  inda kuma Faisal da mahifinsa suka cire kuɗaɗen  tsakanin Oktoban 2013 zuwa Yunin 2019.

Mai shari’ar ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 14 ne kan laifuka biyu sai kuma shekara goma kan laifuka biyu.

An yanke wa Faisal hukuncin shekara 24 ne amma zai yi zaman gidan kaso na shekara 14 ne.

To sai dai Faisal bai halarci zaman kotun ba, inda ake zargin ya gudu zuwa wata kasar waje.