Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da karar da Sanata Danjuma Goje ya shigar domin kalubalantar korar da kwamitin jami’yyar APC na mazabar Kashere da ke jihar Gombe ya yi masa.
Kwamitin dai ya dakatar da Danjuma Goje ne, amma daga baya ya kore shi daga jam’iyyar APC kwata-kwata a watan Afrilu na shekara ta 2023.
Rahotanni sun ce, Kwamitin ya kori Danjuma Goje ne bisa zargin kin shiga ayyukan gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a dukkan matakai, ciki kuwa har da na shugaban kasa tare da yi wa ‘yan takarar majalisar dikoki na jihar da na tarayya zagon kasa.
An kuma zargi Danjuma Goje da kin yi wa shugabannin jami’yyar da’a da kuma kin yin biyayya ga mahukuntan da ke jagorantar jam’iyyar.
Bisa wannan dakatarwa da kuma korar ne ya sa Danjuma Goje ya garzaya zuwa kotun domin kalubalantar matakin, sai dai a hukuncin da alkalin babbar kotun da mai shari’a Obiora Egwatu ke jagoranta ta zartar, ta yi fatali da karar da Danjuma Goje ya shigar.














































