Home Labaru Korona Ta Kashe Karin Mutum Shida A Najeriya

Korona Ta Kashe Karin Mutum Shida A Najeriya

66
0

Mutum shida ne suka rasu a Najeriya ranar Lahadi sakamakon cutar korona, a cewar alƙaluman hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.

Rahoton da NCDC ta wallafa ya nuna cewa ƙarin wasu mutum 573 sun harbu da cutar.

Mutanen sun fito ne daga jiha bakwai na ƙasar. Su ne:

Legas (281), Benue (202), Kano (61), Borno (20), Jigawa (5), Edo (2), Oyo (2)

Ya zuwa yanzu jumillar mutum 243,450 ne suka kamu da cutar a Najeriya yayin da ta yi ajalin mutum 3,039.